Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana cewa, 'yan fashin tekun Somaliya sun sako wasu masunta 26 'yan yankin Asiya da suke tsare da su na kusan shekaru 5.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce gwamnatin kasar Sin tana bayyana godiyarta ga dukkan hukumomi da daidaikun jama'a da suka shiga tsakani game da sakin mutanen.
Madam Hua ta kara da cewa, a cikin watan Maris din shekarar 2012 ne, 'yan fashin tekun Somaliyan suka kama mutane 26 da ke cikin jirgin kamun kifin mai suna Naham 3. A kuma ranar Asabar ne agogon birnin Beijing na kasar Sin aka yi nasarar ceto su, kana daga bisani aka kai su kasar Kenya a jiya Lahadi tare da taimakon hukumomin MDD.
Bayanai na nuna cewa, an yi garkuwa da masunta 29 da ke cikin jirgin ruwan kamun kifi na Naham 3 ne a lokacin da aka kwace tutar jirgin nasu a gabar ruwan kudancin Seychelles, ciki har da masunta 10 daga babban yankin kasar Sin, da 2 daga yankin Taiwan, da wasu 17 daga kasashen Philipines, da Indonesiya, da Vietnam, da kuma Cambodia.
Sai dai kuma Madan Hua ta ce, mutane uku daga cikinsu sun mutu bayan da aka yi garkuwa da su, ciki har da mutum guda daga babban yankin kasar Sin, da kuma guda daga yankin Taiwan.
Yanzu haka dai ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta tura wata tawaga zuwa kasar Kenya, don ganawa da Sinawan da aka ceto. Kuma da zarar an duba lafiyarsu, za a dawo da su gida ba tare da wani bata lokaci ba domin su gana da iyalansu .
Madam Hua ta kuma mika sakon ta'aziya ga iyalan mutane ukun da suka mutu bayan da aka yi garkuwa da su. Tana mai cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi allah-wadai da gallazawar 'yan fashin tekun, wanda hakan cin zarafin bil-Adama ne.(Ibrahim)