in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tattauna matsalar 'yan fashin mashigin tekun Guinea a taron kwamitin sulhun MDD
2016-04-26 10:25:28 cri

A jiya Litinin ne wakilan kasashe mambobin kwamitin sulhun MDD, suka gudanar da taron muhawara kan matsalar 'yan fashin teku a gabar tekun Guinea, inda bayan taron, aka zartas da sanarwar shugaba, wadda ta jaddada cewa, kamata ya yi kasashen duniya su yi kokari matuka wajen daukar matakai tare, ta yadda za a kawo karshen laifuffukan fashi, da sace kayayyaki da makamai a gabar tekun Guinea.

A yayin zaman, wakilin kasar Sin ya yi kira ga al'ummar kasashen duniya, da su kara maida hankali kan kalubalen da kasashen dake gabar tekun Guinea ke fuskantar a fannin yaki da kalubalen tsaro.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China