in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire na shirya atisayen soja domin yaki da 'yan fashin teku
2015-03-27 10:48:01 cri

Hukumomin kasar Cote d'Ivoire sun shirya atisayen soja domin kiyaye tsaron bakin gabobin ruwan kasar, a cewar wasu majiyoyin tsaro a ranar Alhamis.

A cewar manyan jami'an sojan kasar, wannan wata dama ce ta karfafa aikin sanya ido da kuma baiwa jami'an tsaro kayan aiki da nufin fuskantar ayyukan 'yan fashin teku yadda ya kamata.

Wannan atisayen soja da ya samu taimako daga kasar Amurka, zai taimaka wa kasar Cote d'Ivoire kara kyautata tsaron yankin ruwanta, in ji babban komandan ruwa kasar Djakaridja Konate.

A cewarsa, wadannan ayyuka da suka samu halartar jiragen ruwa da dama da jiragen ruwan sintiri na rundunar sojojin ruwa za su taimakawa kasar kimanta karfinta na aiki a wannan fanni. Bisa karuwar ayyukan da ke sabawa doka a cikin ruwan teku, irin wadannan ayyukan atisayen soja na kasancewa wasu makamai na yaki da wannan annoba, in ji kaftin Amara Kone. Haka kuma a cewar ofisan wannan atisayen ya taimaka sosai wajen karfafa dangantaka tsakanin kasashen dake yankin tekun Guinea.

Yankin ruwan tekun Guinea ya yi fama da ayyukan 'yan fashin teku a watannin baya baya. Bisa ga wadannan hare hare na 'yan fashin teku masu dauke makamai, kasashen yankin suke kokarin daukar matakan tsaro na musammun domin murkushe wannan matsala. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China