Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Wang Min ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na son ci gaba da inganta hada kai da musayar bayanai tare da kasashen duniya bisa radin kansu kuma cikin adalci wajen yaki da 'yan fashin teku.
Mista Wang ya bayyana haka ne a yayin cikakken taro karo na 18 da kungiyar tuntuba kan batun yaki da 'yan fashin tekun Somaliya ta shirya. Ya kuma kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan yaki da 'yan fashin tekun Somaliya bisa dokokin kasa da kasa da kuma iznin MDD. Kana kuma tana hada kai da kasa da kasa karkashin shugabancin kungiyar tuntuba kan batun yaki da 'yan fashin tekun Somaliya.
A watan Nuwamban bana ne, ake sa ran kwamitin sulhu na MDD zai tattauna batun tsawaita wa'adin ba da iznin yaki da 'yan fashin teku, kuma wajibi ne a yi la'akari da wasu fannoni. (Tasallah Yuan)