Rundunar sojojin ruwa ta Najeriya, ta kaddamar da wani aikin sintiri da jiragen ruwan yaki 10, a wani mataki na yaki da 'yan fashin teku dake addabar masu safara a sassan ruwayen kasar daban daban.
Mahukuntan rundunar dai sun ce, hakan zai kawo karshen ayyukan masu lalata kayayyakin hakar danyen mai da iskar gas, da ma sauran bata gari da suka zamewa kasar kadangaren bakin tulu.
Da yake karin haske game da hakan yayin kaddamar da shirin a ranar Asabar, babban hafsan dakarun sojin ruwan kasa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya ce, aikin sintirin kari ne kan shirin farko da aka kaddamar, a watanni uku na farkon wannan shekara, da nufin yakar 'yan fashin teku.
Ibo-Ete Ibas ya ce, tsakanin watan Janairu zuwa Afirilun wannan shekara, 'yan fashin teku sun kaddamar da hare hare kimanin 30, wanda kuma suka samu nasara a 16 daga cikin su.
Kaza lika Mr. Ibas ya ce, baya ga kyautata yanayin tsaro a yankunan Niger Delta, aikin sintirin da suka kaddamar, zai baiwa 'yan kasuwa damar safarar hajojin su ba tare da wata damuwa ba, wanda hakan zai dada inganta yanayin tattalin arzikin kasar.
Ya ce, tuni rundunar sa ta shirya tura karin wasu kananan jiragen ruwan yaki 30, domin fadada ayyukan tsaro a sassan yankin Niger Delta mai arzikin mai, duka dai da nufin tabbatar da doka da oda.(Saminu)