in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tenis: An fitar da Djokovic yayin da Murray ya kai wasan karshe
2016-10-19 15:45:16 cri
Roberto Bautista Agut ya fitar da mai rike da kambin gasar Tenis Novak Djokovic daga gasar Shanghai Masters, a wasan kusa da na karshe da suka buga a ranar Lahadi.

Kafin hakan dai Roberto Bautista Agut ya samu nasarar doke Gilles Simon, matakin da ya ba shi damar kaiwa ga wasan karshe a karo na biyu a jere a gasar da ake gudanarwa a nahiyar Asiya.

A daya hannun kuma Murray na ci gaba da kasancewa kan gaba cikin wasannin karshe 10 da ya buga a baya bayan nan, bayan da a makon da ya gabata ya lashe gasar Beijing Open, matakin da ya bashi damar sake rage tazarar dake tsakanin sa da Djokovic a jerin 'yan wasan Tenis mafiya kwarewa a duniya.

Duk dai da kwarin gwiwa da Murray ke da shi na shigewa gaba a harkar kwallon Tenis, ya shaidawa kafar Sky Sports cewa, cimma wannan buri nasa a bana zai yi matukar wuya. Ya ce rashin nasarar Djokovic ta taimaka masa dagawa matsayi na gaba, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba, don haka ba ya hangen cimma burin zama na daya a yanzu ko wani lokaci a nan kusa.

Bautista Agut, wanda ya kai ga wasan karshe a karo na biyu a jere, cikin wasanni 5 da suka buga a baya, bai taba samun nasara kan Djokovic ba, in ban da wannan karo da suka tashi 6-4 6-4 a wasan na ranar Lahadi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China