161013-Najeriya-ta-doke-Zambiya-a-wasan-share-fagen-cin-kofin-duniya-zainab.m4a
|
Najeriyar ta yi nasarar zara kwallayenta biyu ne bayan da dan wasan gaban Arsenal Alex Iwobi ya zara kwallon farko mintoci 32 da fara wasan, yayin da dan wasan gaba na Manchester City Kelechi Iheanacho ya zara kwallo ta biyu mintoci 42 da fara wasa a filin wasa na Levy Mwanawasa dake Ndola city a lardin Copperbelt domin neman shiga gasar ta cin kofin duniya.
Sai dai Zambiya ta rage radadin cin da aka yi mata mintoci 70 da fara wasan ta hanyar dan wasan gaban Afrika ta kudu Collins Mbesuma.
Wadanda zasu kara a rukunin B sun hada da Cameroon da Algeria.
Cameroon sun yi kunnen doki da Algeria da 1-1 a wasannin share fagen kofin duniya a shekarar 2018.
Kociyan Algeria Serbian Milovan Rajevac ne ya jagoranci bude wasan, yayin da dan wasan tsakiya na kungiyar wasan El Arbi Hillal Soudani ya zara kwallo mintoci 7 da fara wasan, kafin daga bisani Benjamin Moukandjo ya zara tasa kwallon daga bangaren Indomitable Lions mintoci 17 da fara wasan inda suka tashi kunnen doki.
Za'a gudanar da zagaye na biyu na rukunin B a ranar 12 ga watan Nuwamba, inda Najeriya zata karbi bakuncin Algeria, yayin da Zambiya zata tashi zuwa birnin Yaounde domin karawa da jamhuriyar Cameroon.
Shugaban Najeriya ya yabawa babbar kungiyar wasan kasar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa kungiyar wasan kwallon kafan kasar sakamakon galabar data samu kan takwararta ta kasar Zambiya a wasan neman shiga gasar kwallon kafa ta duniya da za'a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018.
Cikin wata sanarwa daya fitar a jiya Litinin, shugaba Buhari, ya yabawa 'yan wasan na Super Eagles bisa nasarar da suke samu kan kungiyar wasa ta Chipolopolo ta kasar Zambiya da ci 2-1 a filin wasa na Ndola.
Shugaban na Najeriya ya bayyana nasarar da cewa abin a yaba ne, ya kara da cewa, alamu ne dake nuna yiwuwar samun makoma mai kyau a nan gaba.
Ya bukaci yan wasan da su zage damtse domin kai bantensu domin samun nasarar shiga gasar cin kofin ta duniya.
Najeriya zata bude sansanin horas da yan wasan kwallon kafa kwararru na nahiyar Afrika ajin mata
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya tace a wannan mako zata bude sansanin horas da zakarun yan wasan kwallon kafa ajin mata na nahiyar Afrika domin shirye shiryen shiga gasar kwallon kafa ta zakaru mata ta nahiyar Afrika karo na 10, wanda za'a gudanar a wata mai zuwa a kasar Cameroon.
Hukumar kwallon kafan Najeriyar tace tuni kociyar dake horas da 'yan wasan Florence Omagbemi, ta zabo fitattun 'yan wasa 30, kuma daga cikinsu 22 mazauna kasar ne, yayin da 'yan wasan 8 ke zaune ne a kasashen ketare wadanda a halin yanzu suke Abuja babban birnin kasar domin halartar wasannin.
Asisat Oshola, 'yar wasan jakaru mata ta Afrika wadda ta samu lambar yabo ta gwarzuwar shekara, wacce take buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta mata ta Arsenal dake Ingila, tana daga cikin yan wasan ketare inda ta amsa goron gayyatar kungiyar wasan ta Najeriya.
Za'a fafata a gasar cin kofin kwararru ta Afrika ajin mata ne daga ranar 19 ga watan Nuwamba xuwa 3 ga wata Disambar wannan shekara.