Wata kafar watsa labaran kasar ta ce 'yan wasan Irana Ahmad Esmaeilpour, da Mahdi Javid ne suka ciwa kasar ta su kwallaye biyu-biyu, yayin da a bangaren Paraguay 'yan wasan ta Francisco Martinez, da Juan Salas da kuma Rene Villalba, suka ciwa kasar su kwallaye daya-daya.
Yanzu haka dai Iran din za ta kara ne da kasar Rasha a wasan kusa da na karshe. Gabanin hakan Iran ta doke Brazil a bugun daka kai sai mai tsaron gida a zagayen kungiyoyi 16 na gasar.
Ana buga wannan gasa ta bana ne dai tsakanin ranekun 10 ga watan Satumba zuwa 1 ga watan Oktobar dake tafe, kuma kungoyin zakarun kasashen nahiyoyi daban daban ne ke shiga gasar wadda ke gudana duk bayan shekaru 4 . (Saminu Alhassan)