in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Busquets ya sabunta kwantiragi a Barcelona
2016-09-28 19:46:05 cri
Kungiyar kwallon kafar Barcelona dake Sifaniya ta bayyana sabunta kwantiragin dan wasan tsakiyar ta wato Sergio Busquets, ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2021, tare da damar sake tsawaita hakan da wasu karin shekaru biyu.

Busquets dai bugawa Barcelona wasanni 390 tun bayan da ya kammala samun horo da tawagar matasan kulaf din. Cikin wasannin da ya buga, ya samu nasarar lashe kofuna 6 na kalubale, da kofuna 3 na zakarun turai da kuma kofuna 4 na sifaniya da ma kofunan gasar Super cup.

Ga alama dai dan wasan zai kammala harkar sa ta kwallo a kulaf din wanda ya fara takawa leda tun a watan Satumbar shekarar 2008.

A wasan da Barcelona ta tashi kunnen doki 1 da 1 ita da Atletico Madrid a ranar Laraba, an sauya Busquets mintuna 5 bayan hutun rabin lokaci, sakamakon zazzabi da ya yi fama da shi, sai dai ana fatan zai buga wasan da Barcelonan za ta buga da Sporting Gijon a daren ranar Asabar ,a wasan mako na 6 na kakar wasanni da aka fara.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China