in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya alkawarta tallafawa sashin hada-hadar kudade a Somalia
2015-10-30 09:25:02 cri

Babban bankin duniya ya bayyana aniyarsa, ta tallafawa sashen shige da ficen kudade a kasar Somalia, duba da irin muhimmancin da hakan ke da shi ga tattalin arziki, da ma zamantakewar al'ummar kasar.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Nairobin kasar Kenya, shugaban bankin reshen kasashen Tanzania, da Burundi, da Malawi da kuma Somalia Bella Bird, ya ce, bankin duniya da hadin gwiwar babban bankin kasar Somalia (CBS), na daukar matakan kafa managarcin tsarin lura, da sanya ido domin tabbatar da nasarar musayar kudade a kasar.

Bird ya ce, hakan muhimmin mataki ne, idan aka yi la'akari da cewa kusan kaso 40 bisa dari na iyalan dake rayuwa a kasar ta Somalia, na dogara ne daga kudaden da 'yan uwansu ke aika musu daga ketare. Ya ce, irin wadannan kudade na tallafawa al'umma wajen gudanar da muhimman lamurran rayuwarsu, ciki hadda sayen abinci, da kula da lafiya, da neman ilimi.

Kaza lika, a cewar sanarwar, kaso 80 bisa dari na kudaden da ake amfani da su wajen kafa harkokin cinikayya da kasuwanci na shiga kasar ne daga ketare.

A cikin watanni 18 da suka gabata, masu mu'amala da bankuna a fannin hada-hadar shige da ficen kudade na cin karo da tarin kalubale, gabanin sabbin matakan da bankin na duniya ya alkawarta dauka don shawo kan matsalar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China