in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake nada Kim Yong a matsayin shugaban bankin duniya
2016-09-28 10:57:16 cri
Bankin duniya ya sanar a jiya Talata cewa, daraktocin zartaswarsa sun cimma matsaya kan sake nada Kim Yong a matsayin shugaban bankin, kuma wa'adin aikinsa na biyu zai fara ne a ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2017.

Kaza lika, bankin ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar a wannan rana cewa, daraktocin zartaswar bankin sun gamsu da ayyukan da Kim Yong ya gudanar a wa'adinsa na baya. Kuma sun yaba masa kan ci gaban da bankin ya samu a fannin tafiyar da ayyukansa

A sanarwar da Kim Yong ya fitar, ya bayyana fatansa na ci gaba da hada gwiwa da ma'aikata, abokan aiki da mambobin bankin na duniya domin gina wata duniya mai nuna fahimtar juna wadda babu talauci a cikinta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China