Bangaren dake kula da harkokin masu zaman kansu na bankin duniya, ya sanar a ranar Laraba da niyyarsa ta kara matsayin zuba jari a nahiyar Afrika domin bunkasa tunanin kafa masana'antu.
Daraktan shiyya na kamfanin kudin kasa da kasa IFC reshen gabashi da kudancin Afrika, Cheikh Oumar Seydi ya bayyana a birnin Nairobi cewa, an takaita IFC bisa adadin damammakin da ake da su a Afrika, za mu zuba kudi domin muna da imanin cewa, aikinmu na da muhimmancin gaske a Afrika. Nahiyar Afrika na da manyan bukatu, in ji mista Seydi a dandali kan dabarun saukaka yin harkoki. (Maman Ada)