in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da gudummawa sosai kan ci gaban tattalin arzikin duniya
2016-10-09 10:05:59 cri

Mataimakin ministan kudi na kasar Sin Zhu Guangyao ya furta a shekaran jiya Jumma'a a birnin Washington cewa, asusun IMF ya jinjina sakamakon da Sin ta samu wajen yin gyare-gyare kan aikin samar da kayayyaki, sakamakon da Sin ta samu wajen yin gyare-gyare da neman samun bunkasuwa a dukkan fannoni ya ba da gudummawa sosai kan tattalin arzikin duniya.

Minista Zhu Guangyao dake halartar taron shekara-shekara na lokacin kaka na asusun IMF da bankin duniya ya bayyana wa manema labaru cewa, a gun taron, ya tattauna kan manufofin yin gyare-gyare kan tattalin arzikin Sin tare da mataimakin darektan asusun IMF David Lipton, inda asusun IMF ya jinjina sakamakon da Sin ta samu wajen yin gyare-gyare kan aikin samar da kayayyaki.

Ya yi nuni da cewa, bisa kididdigar da asusun ya yi, an ce, yawan sakamakon gyara tsarin tattalin arziki da Sin ta samu ya dauki kashi 50 ko fiye cikin dari na duk yawan sakamakon da kasashe membobin kungiyar G20 suka samu, hakan ya bayyana cewa, yawan sakamakon da Sin ta samu wajen yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki ya fi dukkan sakamakon da sauran kasashen G20 suka samu yawa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki.

Bugu da kari, Mr. Zhu ya jaddada cewa, asusun IMF ya bayyana kalubalolin da Sin take fuskanta a fannin bashi, alal misali, yawan basusukan da ake bin kamfanonin kasar ya karu cikin sauri. Asusun ya goyi bayan Sin wajen aiwatar da manufofi masu amfani wajen tinkarar wannan batu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China