in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bamako zai karbi bakuncin wani baje kolin bankuna da PME na UEMOA a karshen watan Satumba
2016-08-26 09:57:40 cri
Baje koli karo na biyo na bankuna da kanana da matsakaitan kamfanoni na kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) zai gudana a Bamako, babban birnin kasar Mali, daga ranar 28 ga watan Satumba zuwa ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2016, in ji shugaban kwamitin shirye-shiryen taron, Herman Nagalo a ranar Alhamis a birnin Ouagadougou, a yayin wani taron manema labarai.

Haduwar zata gudana bisa taken "PME a cikin UEMOA gaban bukatun takarar kasa da kasa", kuma tana da manufar kafa wani tsarin musanya na PME bisa tsare tsarensu, da bunkasa dabarun kirkire kirkire ta yadda zasu shiga cikin tattalin arziki domin fuskantar wata takarar kasa da kasa, in ji jami'in.

Fiye da kamfanoni 300 da mahalarta 3000, daga cikinsu akwai kwararru 150, ake sa ran zuwansu a Bamako, in ji mista Nagalo tare da jaddada cewa kasashen UEMOA suna fama da kalubaloli daban daban dake nasaba musammun ma da cigaban masana'antu, tsadar wutar lantarki, karancin abinci, matsalar cigaban birane da kuma wahalhalun samun kudin kafa ayyuka.

A cewarsa, ayyukan PME na taimakawa fiye da kashi 80 cikin 100 na tattalin arzikin wadannan kasashe, suna da sabbin hanyoyin kirkire kirkire, abin da kawai suke bukata shi ne a raka su.

Ana cikin wani yanayin tattalin arzikin duniya na bai daya dake shafar dukkannin tattalin arziki. Masana'antun mu suna fuskantar wata takara mai karfi. African Growth and Opportunity Act (AGOA) na taimakawa kasashen Afrika daban daban gudanar da kasuwancin kayayyakinsu tare da kasar Amurka, amma wannan ba ya amfanawa PME, domin basu samu zarrafin rike wadannan damammaki ba dalilin wasu dokoki, in ji mista Nagalo. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China