Babban kocin Sabtos din Dorival Junior ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata. Alex dan shekaru 34 a duniya, ya kasance dan wasan maras kulaf, tun bayan da wa'adin kwantiraginsa da AC Milan na shekaru 2 ya cika a watan Mayun bana.
A cewar Dorival, babban kocin kungiyar Santos, shi da kulob dinsa suna da sha'awar sanya Alex cikin jerin sunayen 'yan wasansu, sai dai yanzu za a jira a ga ko shi Alex din zai nuna sha'awar zuwa kungiyar ta Santos ko a'a. Ban da haka kuma, a cewar Dorival Junior, yanzu haka shugabannin kulob din Santos na mai da hankali matuka kan wasannin da suke bugawa a kakar wasa ta bana, don haka za su tattauna da Alex daga bisani.
Yanzu haka kungiyar Santos tana matsayi na 4 a teburin gasar fitattun kungiyoyin kasar Brazil, da maki 48 a wasanni 28, wato maki 6 kasa da kungiyar Palmeriras wanda ke kan gaba.
Alex ya fara taka leda ne a kungiyar Santos, kafin ya tafi Chelsea a shekarar 2004. Haka kuma sau 15 yana ciwa kungiyar sa kwallaye 3 a jere a wasanni daban daban da ya halarta tare da kungiyar kwallon kafar kasar Brazil, tun bayan ya fara bugawa kungiyar kasar kwallo a shekarar 2002. (Bello Wang)