in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Saliyo ta sanar da matakan farfado da tattalin arzikin kasar
2016-10-05 12:05:57 cri
Gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da wasu tsauraran matakai da nufin farfado da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare.

Mahukuntan kasar sun bayar da sanarwar ce, bayan da majalisar zartarwar kasar ta kammala wata ganawar gaggauwa a ofishin shugaban kasa, domin lalubo hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasar.

Shugaba Ernest Koroma ya shaidawa majalisar zartarwar kasar cewa, za a aiwatar da matakan har zuwa rubu'in farko na shekarar 2017 da nufin farfado da tattalin arzikin kasar.

Wadannan mataki dai sun hada da rage kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin da aka kebewa bangaren ayyukan yau da kullum, dakatar da duk wasu manyan ayyuka har illa-masha-allahu,haka kuma gwamnati ba za ta sayi wasu sabbin motoci ba.

Bugu da kari, gwamnati ta sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kudaden da aka kebe don sayen mai da motocin ma'aikatu, sassan da hukumomin gwamnati ke amfani da su, baya ga takaita tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da sauransu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China