in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo na shirin sake maido da hukuncin kisa dalilin karuwar manyan laifuffuka
2016-09-17 12:57:39 cri
Ministan cikin gidan Saliyo, Palo Conteh ya bayyana cewa gwamnati na shirin fara aiwatar da hukuncin kisa domin yaki da karuwar ayyukan kisa da makami dake da nasaba da 'yan daba a baya bayan nan a cikin kasar. Za mu kashe idan gwamnati ta bukaci haka, in ji mista Palo Conteh a kwanan nan. Na kira daraktocin gidajen fursunoni domin su wanke wurin rataye mutane, domin kaucewa rashin aiwatar da hakan idan dama ta samu. Hukuncin kisa na har yanzu cikin dokokin kasar mu, idan aka tabbatar da wani mutum ya aikata laifin kisa, to ba za a nuna wani shakku ba doka zata yi aikinta, in ji ministan. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China