in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu : Babu wani yankin kasar da ya fada hannun dakarun 'yan adawa
2016-10-04 12:45:21 cri
Sojojin Sudan ta kudu sun karyata rahotanni da ake ta yayatawa cewa, dakarun da ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar na daya Riek Machar sun kwace iko da garin Morobo da ke kan iyaka, kimanin kilomita 220 kudu maso yammacin Jiba, babban birnin kasar.

Kakakin rundunar sojan kasar Lul Rui Koang, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, an yi fama da tashin hankali a garin Morobo a 'yan kwanakin baya, amma daga bisani al'amura sun lafa.

Tun farko mai magana da yawun Machar, James Gatdet Dak ya tabbatar da cewa, dakarunsu sun kwace iko da garin Morobo da ke kusa da garin Yei wanda ya yi fama da fadan da ya barke tsakanin dakarun gwamnati da na Machar a farkon watan Yuli

Koda ya ke Koang ya bayyana cewa, sojoji sun bude hanyar Juba zuwa Yei wadda ta hade yankunan Kaya da Morobo da ke kusa da kan iyaka da kasashen Uganda da Jamhuriyar demokiradiyar Congo.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China