in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
HCR ta yi allawadai da karuwar tashe tashen hankali a wani birnin Sudan ta Kudu
2016-10-01 11:49:06 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (HCR) ta yi allawadai a ranar Jumma'a kan karuwar tashe tashen hankali a Yei na kasar Sudan ta Kudu, birnin dake tazarar kimanin kilomita 150 daga kudu maso yammacin babban birnin Juba.

Matsalar tsaro a Yei ta kara tsananta cikin sauri bayan barkewar rikici a Juba a farkon watan Yulin da ya gabata, lamarin da ya tilastawa miliyoyin fararen hula barin gidajensu, in ji HCR a cikin wata sanarwa.

Dakarun dake karkashin shugaba Salva Kiir da wadanda suke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar sun yi kazamin fada a farkon watan Yuli a Juba, lamarin da ya janyo sauran tashe tashen hankali a cikin kasar.

A cewar HCR, wannan ne karo na farko da mazauna Yei, musammun ma manoma, suka zama mutanen da aka kaiwa hari kai tsaye game da tashe tashen hankalin.

Mazauna Yei sun yi magana kan muguwar azabatarwa da ake yi wa fararen hula, har ma da hare hare, da kisan mutane, sace dukiyoyin jama'a da kona gidaje, a cewar HCR.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa mutanen da suka kaura, da kuma mazauna wurin dubu 60 da suka tsaya Yei, suna bukatar agajin jin kai.

Mutanen da suka kaura suna bukatar abinci, kayayyakin bukatun yau da kullum, magunguna, kuma ya kamata yara su shiga makaranta. Kayayyakin abinci sun yi tashin gobron zabo, tare da kayayyakin bukatun da yau da kullum na bacewa cikin sauri a cikin kasuwanni, in ji sanarwar HCR. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China