Mali:Ya kamata a tantance da kuma aiki da ilimi ko hikima wajen murkushe kungiyoyin ta'addanci
Tsohon firaministan Mali Moussa Mara ya ba da shawarar yin aiki da ilimi ko hikima wajen kokarin murkushe kungiyoyin ta'addanci a kasar. A wata tattaunawar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya sanar da cewa yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda na bukatar a tantance, kuma a yi aiki da ilimi domin kungiyoyin sun kafu cikin wasu yankuna da al'ummomi, a dalilin karuwar tashe tashen hankali a arewa da tsakiyar kasar. (Laouali Souleymane)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku