Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Talata cewa, wannan muhimmin mataki ne ga kasar Sin, wanda zai fadada shigar ta tsarin hada-hadar kudi na duniya.
Bayan da aka cimma daidaito kan shigar Sin tsarin na SDR a yayin taron kolin kungiyar G20 na Hangzhou, aka kuma shigar da kudin RMB a cikin tsarin ma'aunin na SDR, tsarin zai kara taka muhimmiyar rawa a fagen hada-hadar kudi ta duniya a nan gaba.
Mr Geng Shuang ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana. (Zainab)