in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin kasar Sin zai taka muhimmiyar rawa a kasuwannin hada-hadar kudi na duniya, in ji gwamnonin manyan bankunan Afirka
2016-06-21 19:35:42 cri
Gwamnonin manyan bankunan kasashen Afirka da ke halartar taro a kasar Tanzaniya, sun bayyana cewa, sanya kudin kasar Sin RMB da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi cikin kudaden da za a rika amfani da su a harkokin kudade na duniya, zai sa kudin na RMB ya taka muhimmiyar rawa a kasuwannin hada-hadar kudi na duniya.

Su ma kwararru kan harkokin tattalin arziki daga kasashe daban-daban na Afirka da ke halartar taron gwamnaonin manyan bankuna daga kasashen gabashi da kudancin Afirka sun yi imanin cewa,sanya kudin kasar Sin da asusun da IMF ya yi wani muhimmin ci gaba a kokarin da ake na hade tattalin arzikin kasar Sin cikin tsarin harkokin kudi na Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China