Ma Kai ya jaddada cewa, yanzu Sin tana gudanar da shirin raya kasa na shekaru 5 na 13, shi ya sa tana maraba da masana daga ketare da su samar da makoma mai kyau tare da jama'ar kasar Sin. Da fatan mafi yawan masanan ketare za su shiga aikin bunkasa kasar Sin, domin kara samar da sabbin kayayyaki a kasar. Bugu da kari, gwamnatin Sin za ta dauki kwararrun matakan shigar da gwanaye daga ketare, da gudanar da tsarin amincewa da mutanen kasashen waje wajen yin aiki a Sin, a kokarin ba da kariya ga iko da moriyar masanan ketare bisa dokoki, da samar da yanayi mai kyau ga ci gabansu.
Ana ba da lambar yabo ta sada zumunci ta gwamnatin kasar Sin ne domin yabawa masanan ketare da suka ba da babbar gudummawar zamanintar da kasar Sin. A bana, masana 50 daga kasashen waje 18 suka sami wadannan lambobi.(Fatima)