Game da shirya wannan zabe, hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Asiya, ta gudanar da taron musamman na wakilan hukumar. An jefa kuri'u game da ajendar taron, kuma yawancin membobi mahalartar taron sun jefa kuri'un kin amincewa. A karshe, an samu kuri'un kin amincewa 42, da kuri'ar nuna amincewa 1, don haka aka soke sauran ayyukan da za a gudanar a gun taron. Daga baya, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya Yarima Salman ya sanar da rufe wannan taro.
A yayin taron gaggawa na kwamitin hukumar wasan kwallon kafa ta Asiya da aka gudanar a baya, Yarima Salman ya bayyana cewa, an samu hadin kai a tsakanin mambobin hukumar wasan kwallon kafar Asiya, da dandalin wasan kwallon kafa na Asiya, kana ya nuna godiya ga membobin hukumar bisa nunawa kasa da kasa ra'ayi na bai daya da suke bi.
A daya hannun kuma, an nada mataimakin shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin Zhang Jian, a matsayin memban kwamitin hukumar wasan kwallon kafar ta Asiya, kuma wa'adin aikin sa ya fara ne daga yanzu zuwa lokacin da ake gudanar da taron mambobin hukumar na nan gaba. (Zainab)