A kwanakin baya ne, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong ta gana da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino a birnin Paris dake kasar Faransa.
A yayin ganawar, Liu Yandong ta bayyana cewa, wasan kwallon kafa ya jawo hankalin jama'ar kasar Sin sosai. Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai ga wasan kwallon kafa yayin da take kokarin raya sha'anin wasanninta. A shekarun baya baya nan, an samu ci gaba kan wasan kwallon kafa a kasar Sin, amma duk da haka akwai gibi sosai a tsakaninta da kasashe da suka shahara a bangaren wasanni a duniya. Yanzu kasar Sin tana kokarin yin kwaskwarima kan harkokinta na wasan kwallon kafa, raya sha'anin wasanni a makarantu. Sin tana fatan hukumar FIFA za ta taimakawa Sin wajen yin kwaskwarima da raya sha'anin wasan kwallon kafa a kasar. Hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin za ta nuna goyon baya ga hukumar FIFA, da bada gudummawa wajen bunkasa wasan kwallon kafa a duniya.
A nasa bangare, Infantino ya bayyana cewa, wasan kwallon kafa ba wasa ne kawai ba, hatta ya kasance batu ne da ya yi tasirin musamman a yanayin zamantakewar al'ummar kasa har ma ga dukkan duniya gaba daya. Kwaskwarimar da gwamnatin kasar Sin ta yi a fannin wasan kwallon kafa tana da muhimmanci matuka, kuma za ta taimaka wajen bunkasa harkokin wasanni a kasar Sin, baya ga muhimmancin da ta ke da shi ga sha'anin wasanni a duniya. Hukumar FIFA tana goyon bayan kwaskwarimar da Sin ta ke aiwatarwa, kana tana son kara yin hadin gwiwa tare da hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin da nuna goyon baya ga yin kwaskwarima don raya sha'anin wasanni na kasar Sin. (Zainab)