in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma sakamako da dama a taron ministocin WTO
2015-12-20 14:00:29 cri

A ran 19 ga wata, an kammala taron ministocin kungiyar kasuwancin duniya ta WTO karo na goma a babban birnin kasar Kenya, Nairobi. Mataimakin shugaban tawagar kasar Sin, kana mataimakin ministan kasuwancin kasar Wang Shouwen ya ce, an cimma sakamako da dama a yayin wannan taro, inda kuma kasar Sin ta ba da babbar gudummawa wajen ciyar da shawarwarin da abin ya shafa gaba, da kuma cimma nasarar shirya taron.

A yayin ganawarsa da 'yan jarida bayan bikin rufe taron, Wang ya bayyana cewa, an gudanar da taron ministocin din a lokacin cikon shekaru 20 da kafuwar kungiyar WTO, kuma wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan taro a nahiyar Afirka. Bisa kokarin da sassa daban daban suka yi, an fidda wara sanarwar taron ministocin WTO, da kuma zartas da wasu kudurori a yayin wannan taro.

A cewa Mista Wang, an amince da shirin raya harkokin cinikin kasa da kasa cikin hadin gwiwa da adalci da kasar Sin ta fidda a yayin taron, wanda ya ba da gudummawa wajen cimma ra'ayi daya a yayin taron. Daga bisani kuma, an nuna yabo ga kasar Sin, domin babban taimakon da ta bayar wajen shigar da kasashe mafi fama da talauci cikin tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China