in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin
2016-08-11 14:44:15 cri

A jiya Laraba ne a fadar shugaban kasa, shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ke ziyara aiki a kasar.

A yayin ganawar tasu, shugaba Kenyatta ya ce, kasarsa na son mayar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka wanda aka gudanar a birnin Johannesburg a matsayin wani sabon babi wajen inganta mu'amalar da ke tsakanin manyan jami'ai da jam'iyyun kasashen 2, da kara azama wajen ganin layin jirgin kasa da ake shimfida a tsakanin Mombasa zuwa Nairobi ya fara aiki cikin hanzari, a kokarin kara hada gabashin Afirka baki daya ta hanyar jirgin kasa, ta yadda kasashen Sin da Kenya da ma kasashen gabashin Afirka za su samu nasara tare.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce, kasar Sin tana da kyakkyawan fatan kan makomar bunkasuwar huldar da ke tsakaninta da Kenya. Tana kuma fatan ci gaba da raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Kenya gaba (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China