Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana a gun taron koli na sauyin yanayi na MDD a jiya Laraba cewa, shugabannin kasashen Sin da Faransa sun bayar da hadaddiyar sanarwa kan sauyin yanayi, wadda ake fatan za ta ingiza yunkurin shawarwari kan sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi da ake sa ran cimmawa.
Ban Ki-moon ya ce, dole ne yarjejeniyar ta kara ilimantar da kamfannoni muhimmancin yin tsimin makamashi, da rage fitar da abubuwan da ke gurbata yanayi na duniya. Ban da haka kuma, dole ne wannan yarjejeniya ta kalubalanci jama'a wajen zuba jari a fannin yin amfani da makamashi masu tsabta, domin gyara tsarin tattalin arzikin duniya da zai yi tsimin makamashi. Ya ce, batun sauyin yanayi na kara yin tasiri a duniya, don haka, ya kamata sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi ta duniya ta kara taka rawa.
Daga ranar 30 ga wannan wata zuwa 11 ga watan Disamba ne za a gudanar da taron sauyin yanayi na MDD karo na 21 a birnin Paris na kasar Faransa. Kasashen Sin da Faransa sun jaddada a cikin hadaddiyar sanarwar cewa, ya kamata a gabatar da yarjejeniyar Paris mai yakini a gun taron bisa tushen adalci, wadda kuma ya kamata ta bambanta nauyin da ko wace kasa za ta dauka bisa la'akari da halin da suke ciki.(Lami)