in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liu Jieyi: Kamata ya yi a jibge sojojin wanzar da zaman lafiya bayan yin cikakkun shawarwari da gwamnatin Sudan ta Kudu
2016-08-13 13:59:58 cri
A jiya Jumma'a 12 ga wata, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Liu Jieyi ya bayyana cewa, a yayin da ake shirin jibge sojojin wanzar da zaman lafiya a shiyyar, kamata ya yi a yi shawarwari sosai da gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta Kudu. A wannan rana, kasar Sin ta janye jiki daga jefa kuri'a kan daftarin kudurin kwamitin sulhu dake shafar wannan batu.

A wannan rana, kwamitin sulhun MDD ya jefa kuri'a kan daftarin kudurin da aka kyautata bisa bukatun tawagar musamman ta MDD kan batun Sudan ta Kudu, inda aka zartas da kudurin bisa kuri'ar amincewa 11, da kuri'ar janye jiki 4. Kasashen Sin da Rasha da Masar da kuma Venezuela sun jefa kuri'ar janye jiki. Zaunannen wakilin Sudan ta Kudu a MDD, Bona Malwal ya bayyana bayan zartas da kudurin cewa, wannan kuduri bai yi la'akari da ra'ayin gwamnatin Sudan ta Kudu ba kan batun jibge sojojin wanzar da zaman lafiya a shiyyar da sauran wasu batutuwa, shi ya sa gwamnatin kasar ba za ta amince da kudurin ba.

A cikin jawabinsa, Liu Jieyi ya bayyana cewa, game da batun Sudan ta Kudu, kasar Sin tana fatan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar cikin sauri, da sassauta illolin da yanayin Sudan ta Kudu ke kawo wa kasashen dake wannan shiyya yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China