Ministar kudin kasar Kemi Adeosun ce ta bayyana hakan ga manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar, bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar. Bayanan ministar dai na zuwa ne bayan da hukumar kididdigar kasar ta fitar da wasu alkaluma a ranar Laraba wadanda ke nuna cewa, tattalin azrikin Najeriyar ya yi kasa da kaso 2.06 cikin 100 a rubu'in na biyu na shekara.
Sai dai kuma ministar kudin ta karya zargin da wasu ke yi cewa, masu tsara manufofin tattalin arzikin kasar sun rude kuma ba za su iya ceto tattalin arzikin kasar ba.Ta kuma ce akwai alamar haske a tattalin arzikin kasar.
Shi ma shugaban majalisar 'yan kasuwa da masana'antu reshen Abuja, Tony Ejinkeoye ya ce, karayar tattalin arzikin da kasar ta ke fuskanta ya haifar da rashin aikin yi da wasu tarin matsaloli, kuma lamarin ka iya shafar bangaren ilimi,harkar zuba jari da sauran kananan sana'o'i.
A saboda haka, ya ce, akwai bukatar gwamnati ta gaggauta daukar kwararan matakan da suka dace don magance wannan matsala.
A nasa bangaren babban sakataren kungiyar kwadago ta Najeriya Peter Eson-Ozon, ya jaddada bukatar yiwa manufofin kasar gyaran fuska, ta yadda za a magance halin da tattalin arzikin kasar ya tsinci kansa a ciki.(Ibrahim)