in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijan Najeriya za ta bincike jami'an gwamnatin game da rikicin tattalin arzki
2016-09-15 12:06:12 cri
Majalisar dattijan Najeriya ta yanke shawarar gudanar da bincike kan kusoshin gwamnatin kasar masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arzkin kasar, a matsayin wani mataki na lalubo bakin zaren warware rikcin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a halin yanzu.

Shugaban majalisar dattijan kasar Bukola Saraki, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce da zarar majalisar ta koma bakin aiki a makon gobe bayan da ta shafe makonni 6 tana hutu, za ta fara aikin binciken.

Saraki ya ce, za su bukaci sanin dalilan da suka sa ba'a aiwatar da batun ranto kudade daga kasashen waje, da dalilan da suka hana matakin rage darajar kudin kasar yin tarisi ga ci gaban tattalin arzikin kasar, da kuma dalilan da suka haddasa tashin gwauron zabi wajen musayar kudaden waje.

Ya ce, idan majalisar ta kammala aikinta, za ta gabatar da shawarwari ga shugaba Muhammadu Buhari don aiwatar da su, a matsayin matakai da za su warware matsalar tattalin arzikin kasar.

Najeriya na fuskantar rikicin tattalin arziki ne, tun bayan da hukumar kididdiga ta kasar ta bada rahoto a ranar 31 ga watan Augusta na wannan shekara, game da raguwar ma'aunin tattalin arziki na GDP ya samu a watanni 3 na biyu na wannan shekara da kaso 2.6, bayan da ya ragu da digo 4 kacal a watanni ukun farko na wannan shekara. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China