in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei ya taimakawa 'yan sandan Najeriya wajen kafa wata cibiyar tattara bayyanai
2016-09-02 10:56:28 cri

A jiya Alhamis ne, kamfanin Huawei na kasar Sin da wani kamfanin Najeriya suka hada gwiwa don gina wata cibiyar tattara bayyanai ta 'yan sanda a birnin Abuja, hedkwatar kasar Najeriya. Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo da kuma manajan hulda da jama'a na kamfanin Huawei da ke Najeriya Pan Haiyang da sauran mutane ne suka halarci bikin.

Mista Pan Haiyang ya bayyana cewa, za a gudanar da wannan aiki ne da zummar taimakawa 'yan sandan Najeriya wajen bullo da wani tsari na sadarwa, ciki hadda cibiyoyin tattara bayyanai biyu da ayyukan tattara bayyanan laifuffukan da aka aikata, adana bayyanan masu aikata laifufuka, da binciken hoton yatsun hannu, ofisoshin 'yan sandan kasar fiye da 400 ne za su yi amfani da wannan tsari. Wannan mataki zai taimakawa 'yan sandan kasar wajen kara kwarewarsu ta gudanar aiki.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce, yana fatan 'yan sandan kasar za su yi amfani da tsarin samar da bayyanai na zamani yadda ya kamata, don kara karfinsu na dakile laifuffuka da kiyaye muradun jama'a. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China