in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage haramcin sayar da kudaden ketare da aka sanyawa wasu bankunan Najeriya
2016-09-01 09:23:13 cri
Gwamnatin Najeriya ta sanar da dage haramcin sayar da kudaden kasashen waje da aka kakabawa wasu bankunan kasar a baya.

Darekta a babban bankin Najeriyar(CBN) Tokunbo Martins ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an yanke wannan shawarar ce bayan wata doguwar tattaunawa da shugabannin bankunan da wannan lamari ya shafa, da cibiyar kula da harkokin bankunan ta Najeriya(CIBN).

Mr. Martins ya ce, bayan tattaunawar, babban bankin kasar wato CBN ya amince da tsare-tsaren sake biyan kudaden da bangarorin biyu suka gabatar masa. A saboda haka, babban bankin kasar ya dage wa wadannan bankuna haramcin sayar da kudaden kasashe waje da aka sanya musu a baya a hukumance.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China