Yan sandan birnin London sun tabbatar da cewa, sama da mutane 300 ne aka damke, yayin da wasu mutane 5 suka samu raunuka a lokacin gudanar da bikin shekara shekara a yankin Notting Hill na kasar Birtaniya wanda aka gudanar a karshen mako.
Dubban mahalarta bikin ne suka tsere a rana ta biyu kuma ta karshe wanda za'a kammala bikin, wanda aka saba gudanrawar a yammacin birnin London, kuma shi ne karo na 50 da fara gudanar da shagulgulan, ya samu halartar makada 60 da masu kayan sauti 38.
Da misalin karfe 7 na yammaci wato karfe 6 agogon GMT a jiya Litinin, jami'ai a yankin Scotland sun bayyana cewa, sun damke mutane 160 a rana ta biyu da fara bikin, bayan kama wasu mutanen 156 a ranar Lahadi.
Mafi yawan wadanda aka kama, ana zargin su ne da mallakar haramtattun kwayoyi da makamai ba bisa ka'ida ba. Wasu da dama daga wadanda aka Kaman, an same su da aikata laifuka fiye da guda. Bugu da kari, 'yan sandan sun kwace wukake kimanin 26 daga hannun.(Ahmad Fagam)