Ya zuwa daren jiya Asabar da misalin karfe 10, agogon wurin, yawan mutanen da suka mutu sakamakon bala'in girgizar kasa ya karu zuwa 291 a tsakiyar Italiya, haka zalika, an saukar da tuta zuwa rabin sanda a kasar domin nuna juyayi ga wadanda suka mutu.
Daga cikin matattu 181 da hukumar Italiya ta bayyana, mutum da ya fi tsufa shi ne mai shekaru 93 da haihuwa, yayin da jaririn da ya fi kankanta shine dan watanni biyar da haihuwa. Masu aikin ceto sun ceto mutane 238 a karkashin buraguzan gine-gine, yayin da aka tsugunar da mutane 2100 wadanda suka rasa gidajensu a wurare na wucin gadi.
Firaministan kasar Italiya, Matteo Renzi ya shelanta a ranar 26 ga wata cewa, an ware ranar 27 ga watan Agusta a matsayin ranar makokin a duk fadin kasar.(Fatima)