Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya mika jaje ga wadanda suka ji rauni da iyalansu da kuma gwamnatocin Sin da Kyrgyzstan, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata.
Bugu da kari, kwamitin sulhun ya jaddada cewa, dole ne a cafke masu aikata laifin da wadanda suka tsara shi da masu daukar nauyinsu.
Haka kuma, kwamitin sulhu ya nanata cewa, ta'addanci kome nau'insa yana kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya. Bugu da kari, duk wurin da aka aikata shi, da duk wanda ya aikata shi, bisa kowane dalili, dukkansu mummunan laifi ne na keta doka.
A safiyar Laraba 30 ga watan Agusta ne, aka kai hari da bama-baman da aka dasa cikin wata mota kan ofishin jakadancin Sin dake Kyrgyzstan, wanda ya haddasa jikkatar ma'aikatan ofishin uku, tare da lalata wasu ofisoshi.(Fatima)