in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin kasar Morocco Muhammad VI ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2013-12-24 16:40:26 cri

Ran 23 ga wata, sarkin kasar Morocco Sidi Muhammad VI ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a birnin Rabat.

Yayin ganawarsu, sarki Sidi Muhammad ya bayyana cewa, kasarsa na mai da hankali sosai wajen raya dangantakar diflomasiyya tare da kasar Sin, tare da nuna yabo ga nasarorin da kasar Sin ta samu wajen raya kasa, inda ya kuma ya yi fatan dorewar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tare da kasar Sin. Ya ce, Kasar Morocco tana fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Sin bisa dukkan fannoni don cimma moriyar juna, kuma suna maraba da zuwan karin kamfanonin kasar Sin Morocco, don ba da taimako wajen samar da kayayyakin more rayuwa a wannan kasa. A sa'i daya kuma, kasar za ta ba da taimako ga kasar Sin a fannin raya hadin gwiwarta da kasashen Afirka da na Turai. Haka zalika, ya kuma yana maraba da zuwan jama'ar kasar Sin kasar Morocco domin yawon shakatawa.

A nasa tsokaci, Wang Yi ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa dangantakar doflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Morocco, dangantakar kasashen biyu ke ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau. Ya ce, Kasar Sin na son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Morocco bisa ka'idojin girmama juna, fahimtar juna, nuna goyon baya da kuma yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Haka zalika, kasar Sin na son tattaunawa tare da kasar Morocco wajen karfafa hadin gwiwar kasashen biyu kan harkokin zuba jari da kuma kyautata yanayin cinikayyar dake tsakaninsu, haka zalika, akwai bukatar yin hadin gwiwa a fannin samar da manyan kayayyakin more rayuwa, da yin musayar ra'ayoyi kan harkokin dake shafar al'adu, aikin koyarwa da kuma yawon shakatawa da dai sauran fannoni, ta yadda za a iya neman ci gaba, da kuma samun bunkasuwar tattalin arziki tare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China