A yayin da yake ganawa da manema labaru, Xi ya bayyana cewa, an tabbatar da burin da ake fatan cimmawa a gun taron kolin na Hangzhou.
An mai da "bunkasa tattalin arzikin duniya mai bude kofa da hada kai ta hanyar bullo da sabbin fasahohi" a matsayin taken taron kolin, inda bangarori daban daban da suka halarci taron sun yi musayar ra'ayoyinsu sosai kan haka, ta yadda suka tabbatar da yadda za a hada kai tsakanin mambobin G20, da kuma burin da za su cimma, tare kuma da matakan da za su dauka, kana sun cimma ra'ayi bai daya kan ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Baya ga haka, Xi ya bayyana cewa, gaba daya bangarori daban daban suna ganin cewa, akwai muhimmanci kwarai da a tinkari hadari da kalubale da ake fuskanta a yanzu, da kuma kiyaye zaman lafiya da zaman karko na duniya.
Abin da ya jawo hankali shi ne bangarori daban daban su cimma daidaito kan zurfafa hadin gwiwarsu a fannin yaki da cin hanci. Xi Jinping ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba kan yaki da cin hanci da neman wadanda suka aikata laifin cin hanci da kudadensu, da tsara ka'idoji a wannan fanni, da kafa cibiyar nazari a wannan fanni, da tsara shirin gudanar da ayyukan hana cin hanci na kungiyar G20 tun daga shekarar 2017 zuwa 2018, da kafa tsarin yaki da cin hanci na duniya ciki har da ka'idoji da tsari da gudanar da ayyuka, ta haka wadanda suka ci hanci ba za su tsira a kasashe membobin kungiyar G20 har ma a dukkan duniya gaba daya ba.
A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta gayyaci kasashe masu tasowa 2 wato Kazakstan da Masar don halartar taron kolin G20 na wannan karo a matsayin baki na musamman. Haka zalika, shugabannin wasu kasashen da suka hada da Laos, Chadi, Senegal,Thailand da dai sauransu, su ma sun halarci taron da ya gudana a birnin Hangzhou, wanda ya kafa tarihi bisa samun mafi yawan kasashe masu tasowa da suka halarci taron tun bayan taron kolin da aka shirya a shekarar 2008. A jawabin da ya gabatar a taron na Hangzhou shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a wajen taron an samar da muhimman shawarwari kan yadda za a raya tattalin arzikin duniya, tare da samun nasarorin da suka dace.( Bilkisu Zainab Bello)