in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CBN ya kara yawan kudaden waje da ya ke baiwa 'yan canji
2016-08-19 10:13:32 cri
Yanzu haka gwamnatin Najeriya ta kara yawan kudaden kasashe da ta ke baiwa 'yan canji a kowanne mako daga dala dubu 30,000 zuwa dala 50,000.

Manajan darektan bankin UBA a Najeriya Kennedy Uzoka ya ce an dauki wannan mataki ne, sakamakon karancin kudaden kasashen waje da 'yan Najeriyar suke bukata a kasuwa.

Uzoka ya ce, kafin a karawa 'yan canjin wadannan kudade da suke karba a bunkunan da aka ba su lasisin samar da kudaden, sai da babban bankin Najeriyar na CBN ya tattauna da kwamitin bankuna da wannan batu ya shafa, sakamakon rahotannin da ya samu na bukatar karawa 'yan canjin kudaden kasashen wajen.

Ya yi imanin cewa, wannan mataki zai taimaka wajen kara samarwa 'yan canjin isassun kudaden kasashe waje, daga bisani kuma ya rage farashin musayar dala a kasuwar canji.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China