A wata sanarwa da babban magatakardan MDD Ban Ki-moon wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Myanmar ya fidda ta musamman ta hannun kakakinsa, ya ce, ya kalli kuri'ar da majalisar dattawa ta kasar Brazil ta kada game da tsige Madam Rousseff daga mukaninta, inda aka rantsar da mukaddashinta Michel Temer a matsayin shugaban kasar.
Haka kuma, Mr. Ban ya yi wa Michel Temer fatan alheri, yana mai imani cewa, kasar Brazil da MDD za su ci gaba da dadadden zumuncin dake tsakaninsu karkashin jagorancin Mr.Temer.
A sa'i daya kuma, Ban Ki-moon ya nuna godiyarsa ga uwargida Rousseff dangane da goyon baya da gudummawar da ta baiwa MDD a lokacin da take shugabancin kasar. (Maryam)