in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen Sin da Brazil
2015-05-20 08:52:14 cri


Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar sa na fatan ci gaba da fadada mu'amala da kasar Brazil, musamman ma a fannin musaya tsakanin manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu, don karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da kara mu'amalar al'adu tsakaninsu, domin dora muhimmanci kan hadin gwiwar sassan biyu a bangaren saka jari a fannonin jiragen kasa, da ma'adinai, da wutar lantarki, da kirkire-kirkire da sauransu.
Mr. Li ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin da ke zantawa da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, a ci gaba da ziyarar aiki da yake yi a kasar.
A nata bangare, shugaba Rousseff, cewa ta yi kasar ta na sa ran kiyaye zumuncin gargajiya tsakanin bangarorin biyu, da karfafa hadin gwiwa ta fuskokin samar da ababen more rayuwa, da hada-hadar kudi, da sadarwa, da aikin gona, da makamashi, da zirga-zirgar sararin samaniyya, da samar da kayayyaki a tsakaninsu, kana za a kokarta wajen nazari da inganta hadin gwiwa tsakaninsu a fannin gina hanyoyin jiragen kasa, wadanda za su hade yankunan tekun Fasific da na Atlantica a nahiyar kudancin Amurka, da kuma raya hadin gwiwar bangarorin biyu ta yadda hakan zai zama wani misali mai kyau, tsakanin kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun daddale "Shirin matakan da za a dauka tare, tun daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2021 tsakanin kasashen Sin da Brazil". Kana sun gane ma idanunsu daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa 35 tsakanin bangarorin biyu.
Bugu da kari kasashen biyu sun fidda hadaddiyar sanarwa game da hadin gwiwar su, da wata sanarwar mai alaka da warware batun sauyin yanayi na duniya. (Bako)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China