Da take amsa tambayoyin daga manema labaran game da sake zaben shugaban kasar mai ci yanzu Madam Dilma Rouseff, Madam Hua ta ce Shugaban kasar Sin Xi Jinping tuni ya riga ya aike da sakon taya murna ga Shugaba Rouseff bisa ga wannan nasara.
Madam Hua ta yi bayanin cewa Kasar Sin ta dade tana dora muhimmanci tare da duba zumuncin dake tsakaninta da Brazil tun da ba yau ba a don haka a shirye take ta kara karfafa wannan zumuncin bisa ga amincewa da juna, kara sabbin hanyoyin yin hulda da juna da kuma daukaka wannan zumunci zuwa wani sabon mataki.(Fatimah Jibril)