in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattawan Brazil ta goyi bayan tsige Dilma Rousseff
2016-09-01 10:55:57 cri
A ranar jiya Laraba, majalisar dattawan kasar Brazil ta kada kuri'ar tsige shugabar kasar Dilma Rousseff da kuri'un amincewa 61 bisa ga kuri'un kin amince guda 20. Wannan na nuna cewa madam Rousseff an tsige ta nan take daga mukaminta na shugabar kasar Brazil, kana kuma mista Michel Temer, dake rike shugabancin kasar na wucin gadi bayan an dakatar da madam Rousseff a cikin watan Mayu, zai zaman shugaban kasa har zuwa karshen wa'adinta a shekarar 2018. Madam Rousseff an kama ta laifin boye gibin kudin kasa ta hanyar wasu kurakurai na kasafin kudi, musammun ma na kawo jinkiri wajen biyan rancen kudi ga bankunan kasar da kuma cin karin basusshuka ba tare da amincewar majalisar dokoki ba. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China