Hollande ya bayyana yayin da yake jawabi a gaban tawagar wakilan jakadun kasashe dake kasar Faransa a wannan rana cewa, an shiga wani mawuyacin hali a tattaunar da ake yi kan yarjejeniyar yin ciniki maras shinge a tsakanin Turai da Amurka. Wannan ya sa, ake fuskantar rashi daidaito sosai a tsakanin Turai da Amurka, kana ba a girmama matsayin kungiyar EU ba. A ganinsa, hanya mafi dacewa ita ce duba hakikanin halin da ake ciki, ba ci gaba da yin tattauna bisa yanayin da ake a yanzu ba.
Sakataren kula da harkokin ciniki da kasashen waje na kasar Faransa Matthias Fekl ya bayyana a wannan rana cewa, kasar Faransa za ta shawarci hukumar kungiyar EU a watan Satumba na bana da nufin dakatar da yin tattaunawa kan yarjejeniyar yin ciniki cikin 'yanci a tsakanin Turai da Amurka. (Zainab)