in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara jefa kuri'ar zaben shugaban kasar Gabon
2016-08-27 17:24:05 cri

A sanyin safiyar ranar 27 ga wata da misalin karfe 7 bisa agogon Libreville, hedkwatar kasar Gabon, an fara jefa kuri'ar zaben shugaban kasar, inda rumfunan zabe guda 2580 suka bude kofa ga masu jefa kuri'a kusan dubu 630.

Kwamitin zaben kasar ya ce, za a kammala kada kuri'a da karfe 6 na yamma a wannan rana, kuma za a gabatar da sakamakon zaben a ranar 30 ga wata. Bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar Gabon, wanda ya fi samun yawan kuri'u shi ne zai zama sabon shugaban kasar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China