in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabon na karbar bakuncin gasar damben Kick-boxing na Afrika a karon farko
2016-06-18 11:51:48 cri
An bude gasar damben Kick-boxing na Afrika a karon farko a ranar Jumma'a a birnin Libreville na kasar Gabon.

Wannan gasar ta kwanaki biyu, dake gudana a karon farko a kasar Gabon ta samu halartar kasashen Afrika guda bakwai. Baya ga Gabon mai karbar bakuncin wasannin, akwai kasashen Kamaru, RD-Congo, Congo, Guinee-Equatoriale, tsibirin Maurice da kuma kasar Maroc. Duk da cewa an yi tsimin zuwan kasashen Najeriya, Benin, Mali da Madagascar daga karshe dai ba su samu zuwa ba bisa wasu dalilai na daban.

Bisa ga kalaman shugaban kungiyar wasan Kick-boxing ta kasar Gabon, Eric Richard Ella Bekale, 'yan wasan kasar Gabon sun shirya sosai domin kare tutar kasarsu dake karbar bakuncin wannan gasa ta farko a nahiyar Afrika.

Daga cikin zaratan 'yan damben Kick-boxing da ake jira a Libreville akwai 'yan kasar Kamaru dake rike da kambun gorzayen gasar yankin IV a bangaren masu shawara da kuma 'yan wasan da suka fito daga kasashen yankin Maghreb, da suka shahara wajen karfin juriya.

Kasar Gabon zata gabatar da 'yan wasan damben Kick-boxing goma sha daya da suka samu horo sosai na tsawon watanni uku. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China