in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CPPCC ya gana da shugaban kasar Gabon
2016-04-12 18:16:36 cri
Jiya Litinin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin wato CPPCC, mista Yu Zhengsheng, wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar Gabon, ya gana da shugaban kasar Ali Bongo Ondimba a birnin Libreville.
A yayin ganawar, mista Yu, ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen biyu su yi amfani da damar kai ziyarar juna tsakanin manyan shugabanninsu, da tsayawa tsayin daka kan kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2, da ci gaba da kokarin fahimtar juna da tallafawa juna a wasu manyan batutuwan dake shafar babbar moriyarkasashen biyu.
A nasa bangaren shugaba Bango ya yi godiya game da goyon bayan da kasar Sin take baiwa kasarsa a fannin cigaban tattalin arziki. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China