Adadin 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da ke kasar Kenya ya karu zuwa dubu 46, inda baki daya yawan mutane a sansanin 'yan gudun hijira Kakuma da ke arewa maso yammacin kasar ya kai dubu 185, adadin da ya wuce karfin tsugunnar da mutane dubu 125, a cewar hukumar 'yan gudun hijira ta MDD a ranar Talata.
Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD, UNHCR ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, karuwar mutane a cikin sansanin ta hadasa cunkoson jama'a da dagula lamarin ba da agajin jin kai.
Tare da zuwan tarin 'yan gudun hijira ko da yaushe, ba da taimako domin ceto rayukan jama'a, musammun ma samar da matsuguni da ayyukan bukatun yau da kullum ga 'yan gudun hijira, shi ne abu mafi muhimmanci, in ji UNHCR a cikin wata sanawar a birnin Nairobi.
A cewar wannan sanarwa, tsare tsaren ba da tallafi ga 'yan gudun hijira a wannan shiyya na fuskantar karancin kudi, an bayyana cewa, UNHCR da abokan hulda na bukatar dalar Amurka miliyan 810 domin kiyaye da taimakawa 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu har dubu 821 da ke kasashen Habasha, Kenya, Sudan da Uganda.
Kasar Sudan ta Kudu, dai ta fada cikin rikicin siyasa da yakin basasa tun a tsakiyar watan Disamban shekarar 2013, tashe tashen hankali sun kara tsanani a 'yan makwannin baya baya nan, inda rikici ya barke a jihohin Unity da Upper Niles, lamarin da ya tilastawa miliyoyin mutane barin muhallinsu domin shiga daji, wurare masu tabo, da ma yankunan da ke wuyar shiga. (Maman Ada)