in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarihin Jean-Marie Faustin Gordefroid de Havelange
2016-08-24 13:32:07 cri

Bikin rufe wasannin Olympics da aka gudanar a karshen makon da ya gabata, wani gagarumin biki ne mai matukar tarihi, wanda ke sanyawa a tuna da 'yan mazan jiya da yawa da suka samar da gudunmowa, don haka yayin da muke murnar kawo karshen wasannin, bai kamata mu manta da wasu shakararrun mazan jiya, da suka taba taimakawa a baya wajen raya wasannin Olympics ba. Daya daga wadannan mutane shi ne Dokta Jean-Marie Faustin Gordefroid de Havelange.

Marigayi Havelange shi ne tsohon shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA. Dan asalin kasar Brazil ya taimakawa birnin Rio sosai wajen samun damar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta wannan karo, ganin yadda ya yi kokari tare da shugaban kasar Brazil na lokacin Luiz Lula da "sarkin kwallon kafa" Pele, wajen nuna shirye-shiryen birnin Rio na karbar bakuncin Olympics shekaru 7 da suka wuce.

A lokacin ya gayyaci al'ummar duniya zuwa Brazil a shekarar 2016, lokacin da hakan zai dace da cikar sa shekaru 100 da haihuwa. Sai dai marigayin bai samu damar ganin bude gasar Olympics ta birnin na Rio da idanunsa ba, domin ya rasu 'yan kwanaki kafin kaddamar da bikin, yana da shekaru 100 a duniya.

An zabi mista Havelange don ya zama shugaban hukumar FIFA ne a shekarar 1974. Daga baya ya yi shekaru 24 yana aiki bisa wannan mukami. Babbar gudunmowar da ya samarwa wasan kwallon kafa ita ce kokarin raya wasan ta hanyar amfani da tsare-tsaren kasuwanci. Manufar da ya dauka ta sanya wasan kwallon kafa ya zama daya daga cikin manyan wasannin da suka fi janyo hankalin jama'a, da samun karbuwa, gami da yawan samar da riba.

Shi dai mista Havelange ya bayyana cewa, lokacin da ya karbi FIFA daga hannun magabacinsa, hukumar tana da wani tsohon gini da kuma kudi dalar Amurka 20 kacal, amma lokacin da ya yi ritaya, hukumar na da kadarorin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 4.

Kafin Havelange ya zama shugaban hukumar FIFA, ya kasance wani shahararren dan wasan kwallon ruwa. Ya kuma taba halartar gasannin wasan kwallon ruwa a gasar Olympics ta shekarar 1952, da ta 1956, a madadin kasarsa Brazil. Kuma abin mamaki shi ne yana buga wasa yana kuma kula da kamfaninsa da darajarsa ta kai fiye da dala miliyan daya a lokacin, haka kuma a dukkan bangarorin 2 ya samu ci gaba sosai.

Zuwa shekarar 1958, an zabi Havelange don ya zama shugaban hadaddiyar kungiyar wasannin motsa jiki ta kasar Brazil. Ya kuma rike wannan mukami har zuwa shekarar 1974, lokacin da ya zama shugaban FIFA. Haka kuma, yayin da yake aiki a matsayin shugaban hadaddiyar kungiyar wasanni ta Brazil, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasarsa ta samu lashe kofin duniya har sau 3.

Bayan da ya zama shugaban FIFA, ya yi amfani da kwarewarsa a fanin kula da kamfani wajen kula da hukumar, inda ya yi kwaskwarima ga tsare-tsaren hukumar don ta zama wani babban kamfani, tare da sanya wasan kwallon kafa ya zama wata sana'ar neman kudi, gami da kokarin tallar wasan a duniya. Ban da haka kuma, ya yi kokarin sanya karin mutane su fara buga kwallon kafa. Matakin da ya sanya yawan kungiyoyi masu halartar matakin karshe na gasar cin kofin duniya ya karu daga 16 zuwa 24, har ma zuwa 32 lokacin da aka shirya gasar a kasar Faransa a shekarar 1998. Haka zalika, ya bada gudunmowa wajen sanyawa a baiwa kasashen dake nahiyoyin Afirka, Asiya da Latin Amurka karin kujeru a gasar.

Yanzu haka dai an kammala wasannin Olympics a birnin Rio lami lafiya, ma iya cewa marigayin burinsa ya cika ke nan. Za a dinga tunawa da wannan babban mutum, da ma gudunmowar da ya samar ga harkokin wasannin motsa jiki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China