Adamu, ya furta hakan ne a lokacin zantawa da kamfanin dillancin labarun Najeriyar (NAN), ina yayi zargin cewa akwai wasu dunbin matsalaloli da suka sha gaban hukumar wadanda suke bukatar a warware su.
Sai dai ya ce bai san ta inda ya kamata a bullowa samun nasarar warware dunbun matsalolin dake addabar hukumar wasan kwallon kafan kasar ba, amma yace dole ne a samu sauyi matukar Najeriyar tana fatar samun nasara a gasar wasannin Olympics a shekarar 2020, wadda za'a gudanar a birnin Tokyo, na kasar Japan.
Ya ce abin da yafi sauki shi ne a manta da batun samun nasara a gasar wasannin Olmpic na Tokyo, saboda a halin yanzu kasar na fama da matsalolin kudade saboda irin yanayin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Yace kafin shiga wasannin, dole ne sai an kebe makudan kudade wajen horas da 'yan wasa, kuma idan har babu kudi, to lamarin ba zai yiwu ba.
Ya ce a lokacin da yake jan ragamar hukumar wasannin kasar, ba ya jiran kudade daga aljihun gwamnati don aiwatar da al'amurran hukumar, saboda a cewar sa, harkar wasanni abu ne na lokaci kuma da zarar ya wuce shi ke nan.